Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.
Zuriyar Shallum, da ta Ater, da ta Talmon, da ta Akkub, da ta Hatita, da ta Shobai, su ne zuriyar matsaran ƙofa, yawan mutanensu duka ɗari da talatin da tara.
Sa'ad da maginan suka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji, firistoci suna nan tsaye saye da rigunansu, suna riƙe da ƙahoni, Lawiyawa kuma 'ya'yan Asaf, suna riƙe da kuge domin su yabi Ubangiji, bisa ga umarnin Dawuda, Sarkin Isra'ila.