Sai Yeshuwa da 'ya'yansa da danginsa, da Kadmiyel da 'ya'yansa, da 'ya'yan Hodawiya, da 'ya'yan Henadad, duk Lawiyawa ne, suka yi shugabancin aikin ginin Haikalin Allah.
A rana ta huɗu, a Haikalin Allah, sai aka ba da azurfa, da zinariya, da kwanoni ga Meremot ɗan Uriya, firist, da Ele'azara ɗan Finehas, da Lawiyawa, wato Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.
Lawiyawa su ne, Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel, Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa. Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.