Ezra 2:1 - Littafi Mai Tsarki1 Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.
Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra'ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra'ila, da raguna tasa'in da shida, da 'yan raguna saba'in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.