Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyu Zuriyar Ara, mutum ɗari bakwai da saba'in da biyar Zuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812) Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyar Zuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittin Zuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyu Zuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da uku Zuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222) Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shida Zuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056) Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗu Zuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwas Zuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da uku Zuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyu Zuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da uku Zuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar.