Ezra 10:18 - Littafi Mai Tsarki18 Ma'aseya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya iyalin Yeshuwa ɗan Yehozadak, su ne firistocin da suka auri mata baƙi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.