Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezekiyel 9:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sa'an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra'ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, ‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ya amsa mini ya ce, “Zunubin gidan Isra’ila da Yahuda ya yi girma ainun; ƙasar ta cika da rashin adalci. Suna cewa, ‘Ubangiji ya yashe ƙasar; Ubangiji ba ya gani.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezekiyel 9:9
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ko ka ga abin da dattawan Isra'ilawa suke yi a cikin duhu? Kowa yana cikin ɗakin zānannun siffofin gumaka, sukan ce, ‘Allah ba ya ganinmu. Ubangiji ya rabu da ƙasan nan’ ”


Duk da haka ka ce, ‘Allah bai san kome ba. Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari'a?’


“Sai ka ƙera surƙa, gama ƙasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi.


Tufafinku sun ƙasantu da jinin marasa laifi, Waɗanda ba ku same su suna fasa gidajenku ba. Amma duk da haka kuna cewa,


Waɗanda suke ƙoƙarin ɓoye wa Ubangiji shirye-shiryensu sun shiga uku! Suna gudanar da dabarunsu a ɓoye, suna tsammani ba wanda zai gan su ko ya san abin da suke yi.


Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu, Allah na Isra'ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”


Mugun mutum yakan ce wa kansa, “Allah bai kula ba! Ya rufe idonsa, ba zai taɓa ganina ba.”


Banda wannan kuma Manassa ya kashe adalai har ya cika Urushalima daga wannan gefe zuwa wancan da jininsu, banda zunubin da ya sa mutanen Yahuza su yi, har suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji.


don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani,


Ya kuma ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Wato mutanen Yahuza ba su mai da aikata abubuwa masu banƙyama nan wani abu ba. Sun cika ƙasar da hargitsi, suna ta tsokanar fushina. Ga shi, suna hura hanci a gabana.(Eze 9.9; Eze 16.26)


Amma ka sa idonka da zuciyarka ga ƙazamar riba, Da zubar da jinin marar laifi, Da yin zalunci da danniya.


An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.


saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.


Sun aikata mugunta a gabansa, Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, Su muguwar tsara ce, karkatacciya,


Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”


“Kin amince da kanki cikin muguntarki, Kina tsammani ba wanda yake ganinki. Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata, Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah, Ba mai kama da ni!’


Maƙiyanta sun zama shugabanninta, Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta. Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahala Saboda yawan zunubanta. 'Ya'yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.


Ba a bin doka, Shari'a kuma ba ta aiki. Mugaye sun fi adalai yawa nesa, Don haka shari'a tana tafe a karkace.


“A lokacin nan, Zan bincike Urushalima da fitilu, Zan kuwa hukunta marasa kulawa Waɗanda suke zaman annashuwa, Waɗanda suke cewa a zukatansu, ‘Ubangiji ba zai yi alheri ba, Ba kuma zai yi mugunta ba!’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ