Ezekiyel 9:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sai ga mutum shida sun taho daga wajen ƙofa wadda take daga bisa wadda ta fuskanci arewa. Kowa yana da makaminsa na kisa a hannu. Tare da su kuma akwai wani mutum saye da rigar lilin, yana kuma rataye da gafaka. Sai suka tafi suka tsaya a gefen bagaden tagulla. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Na kuma ga mutane shida suna zuwa daga kowane gefen ƙofar ta bisa, wadda take fuskantar arewa, kowanne da makamin kisa a hannunsa. Tare da su akwai mutum saye da lilin yana rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa. Suka shiga suka tsaya kusa da bagaden tagulla. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |