Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.
Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra'ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”
“ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’