Ezekiyel 8:1 - Littafi Mai Tsarki1 A kan rana ta biyar ga wata na shida a shekara ta shida ta zaman talala, sa'ad da nake zaune a gidana, dattawan Yahuza kuma suna zaune a gabana, sai ikon Ubangiji Allah ya sauka a kaina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 A shekara ta shida, a wata shida a ranar ta biya, yayinda nake zaune a gidana dattawan Yahuda kuma suna zaune a gabana, hannun Ubangiji Mai Iko Duka ya zo a kaina a can. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”