“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,
Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.
Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.
Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?” Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.” Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.