Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezekiyel 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Ya kai, ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa ƙasar Isra'ila, matuƙa ta yi a kan kusurwa huɗu na ƙasar!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila, “ ‘Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo a kan kusurwoyi huɗu na ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezekiyel 7:2
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?” Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.” Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.


Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a.


Zan mai da bukukuwanku makoki, In sa waƙoƙinku na murna su zama na makoki. Zan sa muku tufafin makoki, In sa ku aske kanku. Za ku yi makoki kamar iyayen da suka rasa tilon ɗansu. Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.


“Yanzu matuƙarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara'anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan ƙazantarki.


Sa'ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra'ila ƙaƙaf ne?”


Ana bin sawayenmu, Don haka ba mu iya tafiya a titunanmu ba. Ƙarshenmu ya yi kusa, Kwanakinmu sun ƙare, Gama ƙarshenmu ya zo.


Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna.


A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.


“Ya ɗan mutum, ka fuskanci Urushalima, ka yi magana gāba da masujadanta, ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra'ila.


“Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra'ila cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba’?


Ƙazantarta tana cikin tufafinta, Ba ta tuna da ƙarshenta ba, Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce, Ba ta da mai yi mata ta'aziyya. “Ya Ubangiji, ka dubi wahalata, Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”


Ƙarshenki ya zo, Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa, Mai yawan dukiya. Ajalinki ya auka.


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra'ila, sa'an nan ya koma Urushalima.


Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata, Zan ga yadda ƙarshensu zai zama. Gama su muguwar tsara ce, 'Ya'ya ne marasa aminci.


Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.


Bayan wannan na ga mala'iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace.


ya kuma fito ya yaudari al'ummai waɗanda suke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato, Gog da Magog, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku.


Kina tsammani za ki yi ta zama sarauniya kullayaumin, Ba ki ɗauki waɗannan al'amura a zuci ba, Ko ki yi tunanin yadda za su ƙare.


Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”


Da yake zan karkashe adalai da mugaye daga cikinta, domin haka takobina zai fito daga cikin kubensa, ya karkashe dukan mutane daga Negeb wajen kudu, har zuwa arewa.


“Kai kuma ƙazantaccen mugu, yariman Isra'ila, ranarka ta zo, lokacin hukuncinka ya yi.


“Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra'ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika,


Taku ta ƙare a wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.


Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa'ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ