Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama'ar Isra'ila, da ya zama kufai marar amfani, haka nan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa'an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”
Zan aukar mata da annoba da jini a titunanta. Waɗanda za a ji musu rauni da takobi Za su fāɗi matattu a tsakiyarta. Za a tasar mata a kowane waje. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”
A ranar bakinka zai buɗe, za ka yi magana da wanda ya tsere, ba kuma za ka zama bebe ba. Da haka za ka zama alama gare su, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”
Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.
Zan rushe garun da kuka shafe da farar ƙasa. Za a baje shi, a bar tushen a fili. Za ku halaka a tsakiyarsa sa'ad da ya fāɗi, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.
Ikona zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya, waɗanda suke kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin mutanen Isra'ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani, ni ne Ubangiji Allah.
Ya kuma ce musu, “Ku ƙazantar da Haikalin, ku cika farfajiya da kisassu, sa'an nan ku tafi!” Sai suka tafi, suka yi ta kashe mutanen da suke cikin birnin.
Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa'ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.
Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa'ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa'an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”
Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa'ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu.
Waɗanda Ubangiji ya kashe a wannan rana, Za su zama daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi makoki dominsu ba, Ba kuwa za a tattara gawawwakinsu a binne ba. Za su zama taki ga ƙasa.
Saboda haka ka kawo wa 'ya'yansu yunwa, Ka bashe su ga takobi, Bari matansu su rasa 'ya'ya, mazansu su mutu, Ka sa annoba ta kashe mazansu, A kashe samarinsu da takobi a yaƙi.
Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”
Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.
A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi.
Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta.
Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.
Sa'ad da na mai da ƙasar Masar kufai, In raba ƙasar da abin da take cike da shi, Sa'ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, Daga nan za su sani ni ne Ubangiji.