Zan aiko miki da yunwa da namomin jeji, za su washe 'ya'yanki. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki. Zan kuma kawo takobi a kanki, ni Ubangiji na faɗa’ ”
ku ji abin da Ubangiji ya faɗa a kan sarkin da ya hau gadon sarautar Dawuda, da a kan dukan jama'ar da suke zaune a wannan birni, wato a kan danginku waɗanda ba a kwashe su zuwa zaman talala ba.