3 Za ka ɗibi gashi kaɗan ka ɗaure a shafin rigarka.
3 Amma ka ɗibi gashi kaɗan ka daure a shafin rigarka.
Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.
Irmiya kuwa ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa, ya zauna tare da shi da mutanen da suka ragu a ƙasar.
Amma ya bar matalauta waɗanda ba su da kome a ƙasar. Ya ba su gonakin inabi da waɗansu gonaki a ran nan.
“In adali da ƙyar ya kuɓuta, Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”
Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”
Amma shugaban sojojin ya bar matalautan ƙasar su zama masu gyaran inabi, da masu noma.
Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa'ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu.
Daga cikin gashi kaɗan ɗin nan kuma, sai ka ɗibi waɗansu ka sa a wuta. Daga nan ne wuta za ta tashi a Isra'ila duka.”