Ezekiyel 5:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa'ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |