4 Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.
4 Manasse zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.
Yanzu fa, a kan waɗannan 'ya'yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra'ubainu da Saminu suke.
Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”
Ubangiji Allah ya ce, “Waɗannan su ne kan iyaka da za su raba ƙasar gādo ga kabilan Isra'ila goma sha biyu. Yusufu zai sami rabo biyu.