Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000) ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma (10,000) ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma (10,000), a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar (25,000). Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa.