Tsawon ɗakin 'yan tsaro kamu shida ne, faɗinsa kuma kamu shida. Kamu biyar ne yake tsakanin ɗaki da ɗaki. Dokin ƙofa kuma da yake kusa da shirayin bakin ƙofar Haikali kamu shida ne.
Sa'an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.