Ezekiyel 38:4 - Littafi Mai Tsarki4 Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi cikin muƙamuƙanka, in fitar da kai, da dukan sojojinka, da dawakai da mahayansu. Su babbar runduna ce saye da makamai, wato garkuwoyi, da takuba a zāre, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara 'yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.