Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama'ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya.
A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.