Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.
Zan maishe ka garun tagulla saboda waɗannan mutane, Za su yi yaƙi da kai, amma ba za su yi nasara a kanka ba, Gama ina tare da kai don in cece ka, in kuɓutar da kai.
Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?” Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji.
Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.
Kamar yadda lu'ulu'u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, haka nan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.”