Ka ce mata, ita wadda take zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da suke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce, “ ‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!
Zuciyarka ta yi alfarma saboda kyanka, Ka lalatar da hikimarka ta wurin nuna darajar kanka. Na jefar da kai zuwa ƙasa, Na tone asirinka a gaban sarakuna don su kallace ka.