Zan yi kuka in yi kururuwa saboda tsaunuka, Zan yi kuka saboda wuraren kiwo, Domin sun bushe sun zama marasa amfani. Ba wanda yake bi ta cikinsu. Ba a kuma jin kukan shanu, Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu sun tafi.
Haka Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Za a yi kuka, a yi kururuwa a titunan birninku saboda azaba. Daga ƙauyuka za a kirawo mutane Su zo su yi makokin. Waɗanda suka mutu, tare da masu makoki da aka ijarar da su.
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir'auna, Sarkin Masar, ka ce, “ ‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al'ummai, Amma kai kada ne a cikin ruwa. Ka ɓullo cikin kogunanka, Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka, Ka ƙazantar da kogunansu.’
Za su yi makoki saboda ke, su ce, “ ‘Ke wadda ake zaune cikinki, kin bace daga tekuna, Ya shahararren birni, wanda yake babba a bakin teku, Ke da mazaunan da suke cikinki, kun sa mazaunan gāɓar teku su ji tsoro!
Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”