A Urushalima ya yi na'urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko'ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske.
A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi.
Zai kashe ya'yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi.
Saboda yawan dawakansa, ƙurar da za su tayar za ta rufe ki. Garunki kuma zai girgiza saboda motsin sojojin doki, da na ƙafafu kamar na keke, da na karusai sa'ad da ya shiga ƙofofinki, kamar yadda akan shiga birnin da garunsa ya rushe.