Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezekiyel 26:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Zai kashe ya'yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Zai kashe mazaunan filin ƙasar da takobi; zai yi miki ƙawanya, ya gina miki mahaurai, sa’an nan ya rufe ki da garkuwoyi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezekiyel 26:8
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi.


A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zadakiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina garu kewaye da ita.


“Ga shi, Kaldiyawa sun gina mahaurai kewaye da birnin da suka kewaye shi da yaƙi. Saboda takobi, da yunwa, da annoba aka ba da birnin a hannun Kaldiyawa, waɗanda suke yaƙi da birnin. Abin da ka faɗa ya tabbata, ka kuwa gani.


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku sassare itatuwanta, Ku tula ƙasa kewaye da Urushalima, Dole in hukunta wannan birni saboda ba kome cikinsa sai zalunci,


Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma'aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun.


Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,


Ya'yanta mata waɗanda suke zaune a filin kasar za a kashe su da takobi, sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”


Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura.


Sukan yi wa sarakuna ba'a, Sukan mai da masu mulki abin wasa. Kowace kagara abin dariya ce a wurinsu, Sukan tsiba ƙasa, su hau, su cinye ta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ