Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.
Ubangiji ya ce, “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki takobi mai kaifi, ka more shi kamar askar wanzami, ka aske kanka da gemunka. Ka auna gashin da ma'auni, don ka raba shi kashi uku.
Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a game da ni, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka a nan gaba.
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.
Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”
Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki. Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”
“Ɗan mutum, sa'ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba,
“Ya ɗan mutum, ka yi annabci a kan annabawan Isra'ila. Ka yi annabci a kan waɗanda suke annabci bisa ga ra'ayin kansu, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji!’
Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne.
“Kai ɗan mutum, kada ka ji tsoronsu, kada kuma ka ji tsoron maganganunsu, ko da ya ke ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya sun kewaye ka, kana kuma zaune tare da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.
Ya ce mini, “Ɗan mutum na aike ka zuwa wurin jama'ar Isra'ila, al'umma mai tayarwa, waɗanda suka tayar mini. Su da ubanninsu suna yi ta yi mini laifi har yau.
Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.
Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”
Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka'idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa,