Ezekiyel 17:3 - Littafi Mai Tsarki3 Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.