“Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.
don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”
Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi.
“‘Za ki zama abin zargi, da abin ba'a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al'ummai da suke kewaye da ke sa'ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa.
“Domin haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa.
Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.