Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezekiyel 10:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da rigar lilin. “Ka shiga ƙarƙashin ƙafafun kerubobin, ka cika tafin hannunka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin, ka watsa bisa kan birnin.” Na kuwa ga ya tafi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da lilin, “Ka shiga cikin da’irorin da suke ƙarƙashin kerubobi. Ka cika hannuwanka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin ka kuma watsar da su a kan birnin.” Yayinda nake dubawa, sai ya shiga.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezekiyel 10:2
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai mala'ikan ya ɗauki tasar nan ta turaren ƙonawa, ya cika ta da wuta daga bagadin ƙona turare, ya watsa a kan duniya, sai aka yi ta aradu, da ƙararraki masu tsanani, da walƙiya, da kuma rawar ƙasa.


A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.


Sa'ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa'ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu.


Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.


Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu, Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.


Sai ga mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda kuma yake rataye da gafaka, ya komo da jawabi cewa, “Na aikata yadda ka umarci ni.”


Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.


Ya sauko ta bisa bayan kerubobi, Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.


“Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa. Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara, Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa, Kursiyinsa harshen wuta ne, Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne.


Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ