Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan 'ya'yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.
Domin haka sa'ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”