Esta 9:30 - Littafi Mai Tsarki30 Aka aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa da suke a lardi ɗari da ashirin da bakwai na mulkin Ahasurus, da kalmomin salama da na gaskiya, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202030 Mordekai kuwa ya aika da wasiƙu zuwa ga dukan Yahudawa cikin larduna 127 na masarautar Zerzes. Saƙon fatan alheri da na tabbaci, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.