Esta 9:3 - Littafi Mai Tsarki3 Dukan sarakunan larduna, da hakimai, da masu mulki, da ma'aikatan sarki, suka taimaki Yahudawa, gama tsoron Mordekai ya kama su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Dukan sarakuna larduna, da hakimai, da gwamnoni da kuma ma’aikatan sarki suka taimaki Yahudawa, domin tsoron Mordekai ya kama su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.
Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama'a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki.