Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 9:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 9:22
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka mai da baƙin cikina Ya zama rawar farin ciki, Ka tuɓe mini tufafin makoki, Ka sa mini na farin ciki.


Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.


Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama'ar Isra'ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi.


Yahudawan da suke zaune a ƙauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.


Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.


“Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.


Ka yabi Ubangiji, ya raina, Kada ka manta da yawan alherinsa.


Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a'aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.


Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ”


Ya yi musu umarni, cewa su kiyaye rana ta goma sha huɗu da ta goma sha biyar na watan Adar a kowace shekara.


Sai Yahudawa suka ɗauka su yi kamar yadda suka fara, da kuma yadda Mordekai ya rubuta musu.


“Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci.


Sai ku yi murna a cikin idin, ku da 'ya'yanku mata da maza, da barorinku mata da maza, da Balawe, da baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, waɗanda suke zaune tare da ku.


Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna.


Don haka ba zan yi shiru ba, Zan raira maka yabo, Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan gode maka har abada.


Amma takubansu za su sassoke su, Za a kakkarya bakkunansu.


Don su ci nasara bisa al'ummai, Su kuma hukunta wa jama'a,


“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama'ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ