Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 9:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ya yi musu umarni, cewa su kiyaye rana ta goma sha huɗu da ta goma sha biyar na watan Adar a kowace shekara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ya sa su yi bikin kowace shekara a ranaku goma sha huɗu da goma sha biyar na watan Adar

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 9:21
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A rana ta goma sha uku ga watan Adar ne suka aikata wannan abu. A rana ta goma sha huɗu suka huta, suka mai da ranar ta zama ta biki, da farin ciki.


Amma Yahudawan da suke a Shushan suka taru a rana ta goma sha uku, da rana ta goma sha huɗu, suka huta ran goma sha biyar, suna biki da murna.


Mordekai kuwa ya rubuta abubuwan nan da suka faru, ya aika da takardun zuwa ga dukan Yahudawa waɗanda suke a dukan lardunan sarki Ahasurus, na kusa da na nesa.


Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.


sai Yahudawa suka ga wajibi ne a gare su, da zuriyarsu, da waɗanda ka tare da su, su kiyaye ranaku biyu ɗin nan ba fashi kowace shekara, bisa ga abin da aka rubuta.


Sa'an nan sarauniya Esta 'yar Abihail, da Mordekai Bayahude, ta ba da cikakken iko a rubuce don ta tabbatar da takardan nan ta biyu game da Furim.


An gama ginin Haikali a ran ashirin da uku ga watan Adar, a shekara ta shida ta sarautar sarki Dariyus.


A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri'a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri'a ta faɗo a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ