Esta 9:16 - Littafi Mai Tsarki16 Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Ana cikin haka, sai saura Yahudawa waɗanda suke lardunan sarki su ma suka taru domin su kāre kansu su kuma sami hutu daga abokan gābansu. Suka karkashe mutum dubu saba’in da biyar amma ba su taɓa dukiyarsu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |