Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 9:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Yahudawan da suke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Yahudawan da suke Shusha suka taru a ran goma sha huɗu na watan Adar suka kuma karkashe mutum ɗari uku a Shusha, amma ba su taɓa dukiyarsu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 9:15
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Su ne 'ya'ya goma na Haman, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa, amma ba su washe dukiyarsu ba.


A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.


Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”


Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba.


Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da suke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma a bisa gumagumai.”


Sai Yahudawa suka taru a biranensu a dukan lardunan sarki Ahasurus, don su tasar wa waɗanda suke so su yi musu ɓarna. Ba wanda ya tasar musu gama tsoronsu ya kama mutane.


Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, “A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma 'ya'yan Haman guda goma. Mene ne suka yi a sauran lardunan sarki? Mece ce kuma bukatarki? Za a yi miki. Mene ne kuma roƙonki? Za a ba ki.”


Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ