Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 9:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari a yardar wa Yahudawan da suke Shushan su yi haka gobe, kamar yadda suka yi yau. Bari a rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma a bisa gumagumai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Esta ta ce, “In sarki ya yarda, yă ba wa Yahudawa da suke Shusha izini su aikata dokan nan gobe kuma, bari kuma a rataye ’ya’ya maza goma na Haman a kan gumagumai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 9:13
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.


kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”


Almasihu ya fanso mu daga la'anar nan ta Shari'a, da ya zama abin la'ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la'ananne ne.”


Yahudawan da suke Shushan kuwa suka taru a rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, suka kashe mutum ɗari uku a Shushan, amma ba su washe dukiyarsu ba.


Sarki kuwa ya bai wa Gibeyonawa su. Sai suka rataye su a kan dutse a gaban Ubangiji. Su bakwai ɗin nan suka hallaka gaba ɗaya. An kashe su a farkon kakar sha'ir.


Sai ka ba mu 'ya'yansa maza bakwai domin mu rataye su a gaban Ubangiji a Gibeya a kan dutsen Ubangiji.” Sarki kuwa ya ce, “To, zan bayar.”


Sarki kuwa ya ce a yi haka ɗin. Sai aka yi doka a Shushan, aka kuwa rataye gawawwakin 'ya'yan Haman guda goma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ