Esta 8:8 - Littafi Mai Tsarki8 Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama'a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki.