Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 8:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sa'an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba'agage ya shirya wa Yahudawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 8:3
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.


Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye. Ya yi kuka, ya roƙi albarka. Ya sadu da Allah a Betel, A can Allah ya yi magana da shi.


Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu'a, ya ce,


Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”


Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”


Ta faɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ya shugabana, bari laifin ya zama nawa. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka kuma yarda ka ji maganar baiwarka.


Bayan waɗannan abubuwa, sai sarki Ahasurus ya gabatar da Haman ɗan Hammedata Ba'agage. Ya fīfita shi bisa dukan sarakunan da suke tare da shi.


Sa'an nan sarki ya ɗauki zobensa na hatimi, wanda ya karɓe a wurin Haman, ya ba Mordekai. Esta kuma ta ba Mordekai gidan Haman.


Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ