Esta 8:15 - Littafi Mai Tsarki15 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Aka kewaye wurin da fararen labule da na shunayya na lallausan lilin, aka ɗaure da kirtani na lallausan lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa da ginshiƙai na sassaƙaƙƙun duwatsu masu daraja. Akwai gadaje na zinariya da na azurfa a kan daɓen da aka yi da duwatsu masu daraja, masu launi iri iri.