Esta 7:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sa'an nan Harbona, ɗaya daga cikin bābānin da yake yi wa sarki hidima ya ce, “Ga shi ma, Haman ya riga ya shirya gungumen itace a gidansa, mai tsayi kamu hamsin, inda zai rataye Mordekai wanda ya ceci sarki ta wurin maganarsa.” Sai sarki ya ce, “A rataye Haman a gungumen.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.” Sai sarki ya ce, “Ku rataye shi a kansa!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |