8 Da sarki ya koma daga lambun fāda zuwa inda suke shan ruwan inabi, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sai sarki ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya a gabana, a gidana?” Da dai sarki ya faɗi haka, sai bābāni suka cafe Haman.
8 Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune. Sarki ya tā da murya da ƙarfi ya ce, “Har ma zai ci mutuncin sarauniya yayinda take tare da ni a cikin gida?” Sarki bai ma rufe baki ba, sai bayin sarki suka rufe fuskar Haman.
Aka kewaye wurin da fararen labule da na shunayya na lallausan lilin, aka ɗaure da kirtani na lallausan lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa da ginshiƙai na sassaƙaƙƙun duwatsu masu daraja. Akwai gadaje na zinariya da na azurfa a kan daɓen da aka yi da duwatsu masu daraja, masu launi iri iri.
Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku, Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma, Da tawali'u za su nuna muku bangirma. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”
Bayan da waɗannan kwanaki sun cika, sai sarki ya yi wa manya da ƙanana waɗanda suke a Shushan, wato masarauta, biki, har na kwana bakwai a filin lambun fādar sarki.
Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci ƙafafu biyu Ko kunne ɗaya na tunkiya daga bakin zaki, Haka nan kuma kima daga cikin mutanen Samariya Waɗanda suke zaman jin daɗi za su tsira.