Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 7:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Gama an sayar da mu, ni da mutanena, don a hallaka mu, a karkashe, a ƙarasa mu. Da a ce an sayar da mu mu zama bayi, mata da maza, da na yi shiru, gama ba za a kwatanta wahalarmu da hasarar da sarki zai sha ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 7:4
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idan ya gamshi sarki, bari a yi doka a hallaka su, ni kuwa zan ba waɗanda suke tafiyar da aikin sarki, talanti dubu goma (10,000) na azurfa, don su sa a baitulmalin sarki.”


Ubangiji zai komar da ku Masar cikin jiragen ruwa, ko da yake na ce ba za ku ƙara tafiya can ba. Can za ku sayar da kanku bayi mata da maza, amma ba wanda zai saye ku.”


Aka ba 'yankada-ta-kwana takardun zuwa dukan lardunan sarki don a hallaka Yahudawa, a karkashe, a ƙarasa su, ƙanana da manya, mata da maza, duk a rana ɗaya, wato ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, a kuma washe dukiyoyinsu.


A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun sayar da salihai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta Waɗanda bashinsu bai kai ko kuɗin bi-shanu ba.


Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.


Esta ta ce, “Haman ne, magabci, maƙiyi, mugu!” Sai tsoro ya kama Haman a gaban sarki da sarauniya.


Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, 'ya'yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duka da haka muna tilasta wa 'ya'yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma waɗansu daga cikin 'ya'yanmu mata an riga an bautar da su, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”


Sai ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro, gama wanda yake neman raina yana neman naka. Ka yi zamanka lafiya tare da ni.”


Yanzu fa ku la'anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.”


In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa'an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa,


Sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya Esta, “Wane ne shi, ina yake, wanda zai yi karambanin yin wannan?”


Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”


Amma da Esta ta zo wurin sarki, sai sarki ya ba da umarni a rubuce, cewa mugun makircin nan da Haman ya shirya wa Yahudawa ya koma a kansa. Shi da 'ya'yansa maza aka rataye su a bisa gumagumai.


Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ