Esta 5:1 - Littafi Mai Tsarki1 A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Dukan barorin sarki da mutanen lardunan sarki sun sani duk wanda ya tafi wurin sarki a shirayi na ciki, ba tare da an kira shi ba, to, doka ɗaya ce take kan mutum, wato kisa, ko mace ko namiji, sai dai wanda sarki ya miƙa wa sandan sarauta na zinariya don ya rayu. Kwana talatin ke nan ba a kira ni in tafi wurin sarki ba.”