Sai Esta ta kirawo Hatak, ɗaya daga cikin bābānin sarki, wanda aka sa ya yi mata hidima, ta aike shi wurin Mordekai, don ya ji abin da ya faru, har ya sa yake yin haka.
Mordekai kuma ya ba Hatak takardar dokar da aka yi a Shushan don a hallaka Yahudawa domin ya tafi ya nuna wa Esta ya sanar da ita, ya kuma umarce ta ta tafi wurin sarki don ta roƙi arziki ga sarki saboda mutanenta.