A kowane lardi inda aka kai umarni da dokar sarki, Yahudawa suka yi babban baƙin ciki, da azumi, da kuka, da makoki. Waɗansu da yawa da rigunan makoki a cikin toka suka kwanta.
A rana ta biyu, sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya sāke ce wa Esta, “Mece ce bukatarki, sarauniya Esta? Za a yi miki. Mene ne roƙonki? Za a ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
Sai sarki ya ce wa sarauniya Esta, “A Shushan, masarauta, Yahudawa sun kashe mutum ɗari biyar da kuma 'ya'yan Haman guda goma. Mene ne suka yi a sauran lardunan sarki? Mece ce kuma bukatarki? Za a yi miki. Mene ne kuma roƙonki? Za a ba ki.”
Sai Esta ta kirawo Hatak, ɗaya daga cikin bābānin sarki, wanda aka sa ya yi mata hidima, ta aike shi wurin Mordekai, don ya ji abin da ya faru, har ya sa yake yin haka.