Gama idan kin yi shiru a irin wannan lokaci, to, taimako da ceto za su zo wa Yahudawa ta wata hanya dabam, amma ke da gidan iyayenki za ku halaka. Wa ya sani ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan maƙami?”
“Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”
Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila.