Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sa'ad da suka yi ta yi masa magana kowace rana, shi kuwa bai kasa kunne gare su ba, sai suka faɗa wa Haman, don su gani ko maganar Mordekai za ta tabbata, gama ya faɗa musu shi Bayahude ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Kowace rana suna masa magana, amma ya ƙi yă yi. Saboda haka, suka faɗa wa Haman game da wannan don su ga ko za a jure da halin Mordekai, gama ya faɗa musu cewa shi mutumin Yahuda ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 3:4
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko da yake ta yi ta yi wa Yusufu magana yau da gobe, amma bai biye mata ya kwana da ita ko su zauna tare ba.


Sai Yunusa ya ce, “Ni Ba'ibrane ne, ina bin Ubangiji Allah na Sama, wanda ya yi teku da ƙasa.”


Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”


Akwai waɗansu Yahudawa waɗanda ka naɗa su su lura da harkokin lardin Babila, wato Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Waɗannan mutane fa, ya sarki, ba su kula da kai ba, ba su bauta wa allolinka ba, ba su kuma yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa ba.”


Duk wanda yake na mutanensa da yake nan Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima ta ƙasar Yahuza don ya sāke gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila, shi ne Allah wanda ake masa sujada a Urushalima.


Sai barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka ce wa Mordekai, “Me ya sa ka karya dokar sarki?”


Sa'ad da Haman ya ga Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba, sai ya husata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ