Esta 3:13 - Littafi Mai Tsarki13 Aka ba 'yankada-ta-kwana takardun zuwa dukan lardunan sarki don a hallaka Yahudawa, a karkashe, a ƙarasa su, ƙanana da manya, mata da maza, duk a rana ɗaya, wato ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, a kuma washe dukiyoyinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai mazanni suka tafi ko'ina da ina a dukan ƙasar Isra'ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta. “Ya ku jama'ar Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya.