Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 2:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Mordekai ne ya goyi Hadassa, wato Esta, 'yar kawunsa, gama ita marainiya ce. Ita kuwa kyakkyawa ce. Sa'ad da iyayenta suka rasu, sai Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Mordekai yana da wata ’yar kawunsa mai suna Hadassa, wanda ya yi reno, ba ta da mahaifi ko mahaifiya. Ita ce yarinyar da aka santa da suna Esta. Kyakkyawa ce ƙwarai. Mordekai dai ya ɗauke ta tamƙar ’yarsa sa’ad da mahaifinta da mahaifiyarta suka mutu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 2:7
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda yake lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta.


Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.


In kasance Uba a gare ku, Ku kuma ku kasance 'ya'yana, maza da mata, In ji Ubangiji Maɗaukaki.”


su kirawo sarauniya Bashti ta zo wurinsa da kambin sarauta, don ya nuna wa jama'a da shugabanni kyanta, gama ita kyakkyawa ce.


Yanzu fa, a kan waɗannan 'ya'yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra'ubainu da Saminu suke.


Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.


Har yanzu dai Esta ba ta bayyana asalin danginta da mutanenta ba, kamar yadda Mordekai ya umarce ta, gama Esta tana yi wa Mordekai biyayya kamar ta yi tun lokacin da yake renonta.


A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta.


Ko kuwa in bar marayu da yunwa sa'ad da nake cin abincina,


Tun suna yara nake goyonsu, Ina lura da su kamar 'ya'yan cikina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ